PDP Ta Musanta Shirin Amincewa Da Jonathan A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na 2027

0 174

Wani tsagin jam’iyyar PDP ya yi fatali da rahotannin da ke yawo cewa ana shirin gudanar da babban taro domin amincewa da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027.

Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar na ƙasa, Jungudo Mohammed, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa shugabancin jam’iyyar bai amince da gudanar da wani taro ko babban zaɓe da ya shafi tsayar da Jonathan takara ba.

A cewarsa, rahotannin da ke yaɗuwa ba su da tushe balle makama, yana mai zarginsu da kasancewa wani yunƙuri na haddasa ruɗani da rikice-rikicen siyasa a cikin jam’iyyar da ma ƙasar baki ɗaya.

Wannan na zuwa ne bayan da wani tsagin kwamitin riƙon ƙwarya na PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya sanar da shirin gudanar da wani babban taro a Abuja domin tabbatar da Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Sai dai jam’iyyar PDP ta jaddada cewa ta bi dukkan matakan da suka dace wajen gudanar da harkokin cikin gida, tare da bin ƙa’idojin INEC da kundin tsarin mulkin jam’iyyar wajen tafiyar da zaɓukan fidda gwani.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga mambobinta da al’umma da su yi watsi da duk wani bayani da ba ya fitowa daga jagororin jam’iyyar da aka sani ba, tana mai cewa za ta ci gaba da kare mutuncinta da bin dokokin dimokuraɗiyya.

Leave a Reply