PDP Ta Shirya Taron Tabbatar Da Mustapha Sule Lamido A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Jigawa Na 2027

0 176

Jam’iyyar PDP a Jihar Jigawa ta sanar da cewa za ta gudanar da taron tabbatar da Alhaji Mustapha Sule Lamido, wanda aka fi sani da Santurakin Dutse, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar domin zaɓen shekarar 2027.

Taron zai gudana ne a ranar Lahadi 24 ga watan Mayun 2026 da misalin ƙarfe 10:00 na safe, a dakin taro na MTown Hotel da ke kusa da Aminu Kano Triangle a kan titin Kiyawa cikin birnin Dutse.

Mustapha Sule Lamido, ɗan tsohon gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, ya kasance ɗan takarar PDP a zaɓen 2023 kuma a baya-bayan nan ya samu goyon bayan wasu shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar.

Leave a Reply