PDP ta yi raddi kan kalaman shugaban kwamatin rikon kwarya na APC

0 106

Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi raddi kan kalaman da abokiyar hamayyarta APC mai mulkin kasar ta yi cewa za ta kwashe shekara 36 tana mulkin kasar.

Shugaban jam’iyyar na riko kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ne ya bayyana haka ranar Talata.

Mai magana da yawun jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya ce ‘yan Najeriya sun shirya tsaf domin fatattakar jam’iyyar APC a shekarar 2023.

PDP ta kara da cewa ko ikirarin da APC ta yi na sabunta rijistar zabe ta ‘yan kasar miliyan 36, shaci fadi ne da babu wani tasiri da zai yi ga ‘yan Najeriya komai ba.

“PDP ba ta yi ko dar ba bisa ikirarin da shugaban riko na jam’iyyar APC Gwamna Mai Mala Buni ya yi, ba mu tsorata da karfin da APC ke ganin tana da shi ba na hukumar zabe da fannin shari’a da gayyato bata-gari daga wasu kasashe domin su taimaka mata wajen dagula lamura a lokacin zabe mai zuwa,” in ji shi.

Ya kara da cewa kalaman Maimala Buni na nufin ‘yan Najeriya su nade hannu su ci gaba da zama cikin kunci da talauci da yunwa da rashin tsaro, da ukuba na karin shekaru 26.

“Wannan rashin tausayi da nuna halin ko in kula ne da bai kamata ‘yan Najeriya su nade hannu su zuba ido da ci gaba da zama cikin wannan halin ba,” a cewar Ologbondiyan.Article share tools

Leave a Reply

%d bloggers like this: