Pentagon Na Neman Karin Dala Biliyan 80 Domin Cike Gibin Kuɗaɗen Yaƙin Iran

0 174

Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) na shirin neman Majalisar Dokokin ƙasar ta amince da ƙarin kasafi na kusan dala biliyan 80 domin biyan kuɗaɗen da ake cewa sun taso daga yaƙin Iran da kuma sauran ayyukan soja, kamar yadda rahoton jaridar Wall Street Journal ya bayyana.

Jaridar Punch ta rawaito cewa mataimakin sakataren tsaro, Stephen Feinberg, ya tattauna batun da wasu ‘yan majalisa a wannan mako, inda Pentagon ya yi gargadin cewa kuɗaɗen da ake da su na iya ƙarewa cikin watanni masu zuwa idan ba a amince da sabon kasafin ba.

Rahoton ya ce wani ɓangare na kuɗin za a kashe shi wajen sayen makamai, biyan albashin sojoji da kuma gudanar da ayyukan jiragen ruwa. A watan da ya gabata, Pentagon ya bayyana cewa kuɗin yaƙin Iran sun kai kusan dala biliyan 29, sai dai masu sukar yaƙin na ganin ainihin kuɗin ya fi haka.

A gefe guda, wasu ‘yan majalisa na matsa lamba kan sai an samu amincewar Majalisa kafin a ware ƙarin kuɗaɗen, yayin da ‘yan jam’iyyar Democrat ke zargin Shugaba Donald Trump da fara yaƙin ba tare da sahalewar Majalisa ba, abin da suke ganin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar.

A ƙarƙashin dokar War Powers Act, shugaban ƙasa na da kwanaki 60 kacal bayan tura dakaru cikin rikicin yaƙi domin neman amincewar Majalisa.

Leave a Reply