Rahoto: Yaya Farashin Raguna Da Shanu A Sallar Layyar Bana?

0 112

Wani binciken kamfanin dillancin labarai na kasa ya nuna yadda farashin dabbobi bai tashi ba a kasuwannin Shuwarin da Sara da Gujungu, duk anan Jihar Jigawa, cikin kasa da sati 1 kafin Sallah.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran, wanda ya zagaya kasuwannin, ya lura yadda farashin raguna da shanu da kaji bai karu ba daga yadda yake a kwanakin baya.

Wasu masu sayar da dabbobin sun bayyana rashin tashin farashin da karancin kudi a hannun mutane

Wani wanda ya kawo ragunansa domin ya sayar, Mallam Ibrahim Umaru, babu wanda ya samu ya taya.

Wani da yake bayani, Mallam Ado Musa, yace ragon da a baya yake kaiwa Naira 35,000 zuwa 50,000, kuma ake sa ran tashin farashinsa, yana nan bai tashi ba.

Sauran masu sayar da dabbobin sunyi bayani makamancin hakan, inda suka ce matsalar data fadawa farashin kayan abinci a wannan shekararr, ita ta shafi dabbobi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: