Farashin Sukari Ya Dauka Hanyar Karyewa A Najeriya

0 377

Gwamnatin Najeriya ta ce nan da shekara ta 2023 za ta fara sarrafa sukari a cikin kasar.

Babban sakataren ma’aiktar bunkasar sukari ta kasa Dr. Latiz Busari ya bayyana hakan a Abuja yayin da yake sanya hannu kan yarjejeniyar noman rake da kamfanonin BUA da kuma NETAFIM.

Busari ya ce yarjejeniyar zata bunkasa harkokin kasuwancin noman rake, ta hanyar samarwa da kamfanonin raken da aka noma.

Sakataren ya kuma yabawa kamfanin na BUA wajen kawo wannan kulla wannan yarjejeniya da hukumar domin samun abin  da ake bukata.

Da yake maida jawabi daraktan kamfanin na BUA Kabir Rabi’u ya ce kamfanin zai samar da jari na kimanin naira bilyan 108 cikin yarjejeniyar a fadin kasar nan.

Kazalika ya ce yarjejeniyar tsakanin kamfanin NETAFIM da BUA zai bunkasa noman rani na kimanin kadada 20,000 a yankin Lafiagi ta hanyar amfani da hanyoyin noma na zamani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: