An Kammala Jigilar Alhazan Nijeriya, Duba Don Sanin Adadinsu

0 134

Hukumar Alhazai ta Kasa ta bayar da sanarwar kawo karshen  jigilar maniyyata daga Najeriya zuwa aikin Hajjin Bana a Saudiyya.

Sanarwar na cikin jawabin da aka bawa kamfanin dillancin labarai, daga hannun shugaban sashen hulda da jama’a ta hukumar, Fatima Usara, jim kadan bayan jigilar karshe a jirgin karshe wanda ke dauke da ma’aikatan hukumar, sa’ilin da suka tashi daga filin jiragen sama Nnamdi Azikiwe dake Abuja, zuwa Saudiyya.

A cewar Fatima Usara, aikin hajjin bana, ya kunshi jigilar alhazai a jirage sau 93, wadanda suka kai alhazai 44,450, daga hukumomin jin dadin alhazai na jishoshi.

Hukumar ta kuma yabawa kokarin hukumomin jin dadin alhazai na jishoshi da sauran masu ruwa da tsaki, domin nasarar aikin da aka samu.

A cewarta, hukumar tana fatan sake samun makamanciyar nasarar da aikin hadin gwiwa, yayin aikin dawo da alhazan gida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: