Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Kasa (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ta bayyana Litinin, 15 ga watan Maris a matsayin daya ga watan Sha’aban na 1442.

Hakan ya biyo bayan rashin ganin jinjirin sabon watan a ranar Asabar, wacce ita ce 29 ga watan Rajab.

anarwar hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Masarautar, kuma Sarkin Malaman Sakkwato, Yahaya M. Boyi ya fitar da safiyar ranar Lahadi.

A ka’idar kalandar Musulunci dai, akan cika wata ya zama kwanaki 30 idan aka gaza ganin jinjirin sabon wata a daren 29 sannan washe gari ta zama daya ga sabon wata.

Watan Sha’aban dai shine wata na takwas a kalandar Musulunci kuma daga shi sai watan Ramadan wanda a cikinsa ne Musulmai a duk fadin duniya ke yin ibadar Azumi tsawon kwanakin watan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: