Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Rayuwa, Girma, Da Ci Gaban Yaran Kasar Nan

0 73

Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya ce rashin abinci mai gina jiki barazana ce ga rayuwa, girma, da ci gaban yaran kasarnan.
Lai Mohammed, wanda babbar sakatariyar ma’aikatar, Lydia Shehu-Jafiya ta wakilta, ya bayyana haka a jiya a wajen kaddamar da kungiyar yada labaran abinci mai gina jiki ta musamman ta kasa a Abuja.
A cewarsa, abinci mai gina jiki yana da matukar muhimmanci wajen cimma muradun ci gaba mai dorewa, da samar da ingantacciyar lafiya da ci gaba, a saboda haka akwai bukatar a tunkari kalubalen magance matsalolin da yake fuskanta.
Ministan yayi nuni da tafiyar hawainiyar da ake samu akan sakamako tare da lura da gibin da ake samu kan zuba jari a bangaren abinci mai gina jiki a kasar nan, musamman a fannin sa ido, tantancewa da gaskiya daga masu ruwa da tsaki.
Ya ce kaddamar da kungiyar ‘yan jarida ta kasa kan abinci mai gina jiki zai taimaka wajen ingantuwa da aiwatar da shirye-shirye akan abinci mai gina jiki a kasar nan, musamman a yankunan karkara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: