Farashin Wutar Lantarki A Najeriya Shine Mafi Araha A Duniya

0 66

Ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu, a jiya, ya ce kudin wutar lantarki a Najeriya shi ne mafi arha a duk duniya.
Ya ce duk da arahar wutar da kuma kokarin gwamnati na samar da wutar ga ‘yan Najeriya, mafiya yawan masu amfani da wutar musamman hukumomin gwamnati, basa biyan kudin wuta.
Ya yi wannan magana ne jiya a Abuja yayin wani zaman ganawa da kwamitin wutar lantarki na majalisar dattawa da kuma shugabannin hukumomi daban-daban a bangaren wutar lantarki.
A nasa jawabin, Manajan Kamfanin Watsa Wutar Lantarki na Kasa, Sulyman Abdulaziz, ya ce rashin biyan kudin wutar lantarki da wasu manyan hukumomin gwamnati ke yi ne ya sa aka yanke wutar ta kamfanonin rarraba wutar lantarki na Kaduna da Kano a kwanakin baya.
Ya ce duk da an sake mayar musu wutar na wani dan lokaci, dole ne su biya kudaden da kamfanin watsa wutar ke binsu cikin kwanakin 60 da aka ba su.
Shugaban kwamatin majalisar, Sanata Gabriel Suswam ya ce daya daga cikin korafe-korafen da Kamfanonin Rarraba Wutar suka yi shi ne tarun basukan da suke bin masu amfani da wutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: