An Yi Ta Harbe-Harbe Da Tayar Da Abubuwa Masu Fashewa A Duk Fadin Birnin Khartoum Na Kasar Sudan

0 62

An yi ta harbe-harbe da tayar da abubuwa masu fashewa a duk fadin birnin Khartoum na kasar Sudan a rana ta 20 a jere ana yaki.

Shaidu sun ba da rahoton karar fashewar abubuwa da kuma musayar wuta a kan tituna.

An kuma samu tashin bama-bamai masu yawa a garuruwan Omdurman da Bahri da ke makwabtaka da birnin..

Rundunar ta ce a shirye ta ke ta yi biyayya ga sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki bakwai, sai dai babu wata sanarwa da ta fito daga kungiyar RSF.

Sojojin sun ce sun kashe mayakan RSF tare da lalata wasu motoci nasu, bayan da suka yi arangama da kungiyar a yankin sojojin na birnin Bahri.

Rahotanni sun ce ana kokarin korar dakarun RSF daga yankin da ke kusa da fadar shugaban kasa da kuma hedkwatar sojoji. Babban jami’in bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths, ya ce jajircewar bangarorin da ke fada da juna suka yi na ci gaba da fada zai iya mayar da rikicin zuwa wani babban bala’i na duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: