Rashin danganata ta kusa tsakanin Jamhuriyar Benin da Najeriya na kawo cikas ga cigaban kasashen biyu

0 166

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yace rashin danganata ta kusa tsakanin Jamhuriyar Benin da tarayya Najeriya na kawo cikas ga cigaban kasashen biyu.

Bola Ahmed Tinubu ya fadi haka ne jiya a Abuja yayinda ya karbi bakuncin takwaran sa na Jamhuriyar Benin Patrice Talon, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaba Tinubu ya tabbatarwa takwaran sa na Benin cewa, gwamnatin tarayya zata cigaba da tallafawa kamfanoni masu zaman kan su domin cigaban kasashen biyu.

Shugaba Talon na jamuriyar Benin, ya je fadar shugaban kasa ne domin neman taimakon shugaba Tinubu na Inganta alakar kasuwancin, gabanin taron koli na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma na ECOWAS,inda ya bayyana alakar Najeriya da Benin a matsayin mai mahimmancin. Shugaba Talon, yace jamhuriyar Benin na neman hada huldar kasuwanci tsakanin ta da Najeriya, yana mai bayyana cewa hakan zai kawo cigaba ga al’umomin kasashen biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: