Rikici ne yasa muka rufe makarantun fulani – Karamar hukumar Guri

0 72

Majalisar karamar hakumar Guri ta rufe makarantun yan Fulani makiyaya da kasuwannin yankin baki daya, a sakamakon rikicin dake cigaba da ta’azzara a yankin tsakanin makiyaya da manoma.

Mazauna yankin sun ce akalla mutane 9 ne aka kashe a sabon rikicin daya faru a yankin da aka fara ranar juma’ar data gabata.

Manema labarai sun rawaito yadda mutane 2 suka rasa rayuwarsu sannan wasu 5 suka tsira da raunuka a yankin.

Rundunar yansanda daga baya ta tabbatar da mutuwar wani mutum a wani kauye dake mokobtaka da karamar hakumar Kirikasamma.

Kakakin rundunar yansandan jihar jigawa DSP Lawan Shiisu Adam yace mutane da yawane da lamarin ya rutsa da suke karbar kulawar likitoci a asibitoci daban-daban a fadin jihar Jigawa.

Yace rundunar yansanda ta kama wasu mutane 10 da ake zargi da hannu a rikicin daya ki ci yaki cinyawa.

Jami’in yada labaran yankin Sunusi A. Doro ya sanar da yan jarida cewa sakataren ilimi na karamar hakumar Sale Kaka ya bada umarnin rufe dukkanin makarantun Fulani dake fadin yankin, biyo bayan barazana da malaman makarantun ke fuskanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: