Hakumar hizba a jihar Jigawa ta kama jarakuna 8 dauke da giyar barasa yar gargajiya da aka fi sani da Burkutu.

Hazba tayi kamen ne a yankin karamar hakumar Maigatari, yayin da ta kwace kwalaben barasar guda 96 a jiya talata.

Babban kwamandan hakumar na jiha Malam Ibrahim Dahiru, ya gayawa kamfanin dillacin labarai na kasa NAN kamen a jiya.

Yace hakumar ta gudanar da sumame da misalign karfe 3 na dare guraren da take zargin ana aikata ayyukan masha’a.

Kwamandan yayi kira ga al’uma da su kauracewa sha da dillacin irin wadannan kayan laifin a fadin jihar jigawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: