Babban banikin kasa CBN yace ya ware sama da naira biliyan 42 domin bunkasa noman alkama a kadada dubu 132, da 799 a jihohi 15 dake fadin kasar nan.

Wannan na kunshe cikin jawabin da gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya yi a wajen bikin kaddamar da shirin girbin alkama daya gudana a kauyen Gabarin na karamar hakumar Ringim a nan jihar jigawa.

Emefiele wanda ya samu wakilcin Hajiya Sa’adatu Ibrahim, babbar mai kula da babban bankin rashen jihar Jigawa, ta bayyana cewa wannan kokari da babban bankin keyi zai kawo karshen kalubalen karanci da hauhawar farashin alkama da ake samu.

Ya bayanin cewa an kirkiri dabarar ne da nufin bunkasa samar da alkama mai kyau ta hanyar amfani da irin alkama da kasashen waje.

a karshen shekarar data gabata ne babban bankin ya kaddamar da rabon kayan aikin noman alkama a kauyen kacallari dake yankin karamar hakumar Malam Madori, kayayyakin da suka hada irin noma, taki, maganin feshi da injin bayi ga monoma.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: