Labarai

Har yanzu ba mu samu adadin mutanen da farmakin yan bindiga ya shafa a jirgin Kasan Abuja zuwa Kaduna ba – Gwamnatin Jihar Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce har yanzu bata samu adadin mutanen da farmakin yan Bindiga ya shafa a Jirgin Kasan Abuja zuwa Kaduna ba.

Manema Labarai sun rawaito cewa yan ta’addar sun sanya Bomb a layi daya na hanyar Jirgin Kasan Abuja zuwa Kaduna wanda hakan ne ya sanya Jirgin tsayawa.

Yan bindigar sun budewa Fasinjojin Jirgin wuta wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar wasu Fasinjojin tare da sa ce wasu da dama.

Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gidan Jihar Kaduna Mista Samuel Aruwan, ya ce an tsinci gawarwakin mutane 8 tare da samun mutane 26 da suka samu raunika kuma suna cigaba da samun kulawar Likitoci.

Gwamnatin Jihar Kadunan ta ce a bayanan da ta samu daga hukumar Jirgin Kasan Najeriya kimanin mutane 362 ne suka hau Jirgin daga Abuja zuwa Kaduna.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: