Shehu ya ce aikin layin dogon bai cikin wani tsari na hukuma da gwamnatin tarayya ta amince da shi, yana mai jaddada cewa babu wani tanadi a kansa cikin shirin kasafin kuɗin shekarar 2026.
A cewarsa, ba a gabatar da wata takarda (memo) ga Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) domin tattaunawa a kai ba, kuma babu wani tsari (design), ɗan kwangila ko mai ba da shawara (consultant) da aka tanada domin aiwatar da aikin.
Shehu ya zargi cewa sanarwar da aka yi an yi ta ne domin yaudarar al’ummar Jihar Kano.
Ya ce:
“Wannan yaudara ce tsantsa. Babu irin wannan tanadi a cikin shirin kasafin kuɗin 2026. Babu wata takarda da aka gabatar wa FEC domin tattaunawa. Babu wani tsari a fili. Babu ɗan kwangila. Babu masu ba da shawara.
“An yi wannan ne kawai domin ruɗar al’ummar Jihar Kano, saboda Abba ya shiga ƙungiyar ‘Gorilla da dabbobi masu dafi’ inda guba ke yawo,” in ji shi.
Martanin nasa ya biyo bayan wata sanarwa da Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya yi, inda ya ce Gwamnatin Tarayya ta amince da aikin Metropolitan Rail Service na naira tiriliyan ɗaya (₦1 tiriliyan) domin jihar.
A tuna cewa Gwamnan Kano ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance. Wannan mataki nasa na ci gaba da haifar da cece-kuce da martani daga sassa daban-daban na ƙasar da kuma cikin Jihar Kano.