Rundunar ƴansanda ta kama wani da yaudarar wani yaro ɗan shekara 9 da yayi garkuwa da shi daga makaranta

0 107

Rundunar ‘yansandan kasarnan a jiya sun ce sun kama wani mutum a Abuja da ake zargi da yaudarar wani yaro dan shekara 9 da ya fito da shi daga makaranta yayi garkuwa da shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yansandan kasarnan, Frank Mba, ya sanar da haka lokacin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja.

Frank Mba yace wanda ake zargin ya yaudari yaron da cewa iyayensa ne suka umarce shi ya tafi da shi zuwa makarantar koyar da komfuta.

Yace wanda ake zargin ya dauki yaron daga makarantar kuma ya boye shi ba tare da duka ko cin zarafi ba.

Frank Mba yace an boye yaron har sai da iyayensa suka biya kudin fansa na naira miliyan 1 da rabi, kamar yadda wanda ake zargin ya bukata.

Yace an samu nasarar kwato yaron wanda aka damka shi ga iyayensa kuma an kama wanda ake zargin tare da kudin fansar da aka biya shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: