Rundunar Sojojin Ƙasa Ta Dakatar da RitayarJami’anta Saboda Yanayin Tsaro a Najeriya

0 570

Rundunar Sojojin Ƙasa ta Najeriya ta dakatar da dukkan ritaya ga jami’anta da suka kai lokacin ritaya, ko wanda suke son su ajiye aiki a radin kansu saboda yanayin tsaro a Najeriya.

Wannan mataki ya biyo bayan sanya dokar ta baci kan tsaro da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana a fadin ƙasar, biyo bayan yawaitar sace mutane a fadin Najeriya, inda aka sace fiye da mutum 600, aka yi garkuwa da su a watan Nuwamba kaɗai, ciki har da ɗalibai sama da 300 a Jihar Neja, 38 masu ibada a Kwara, da ɗalibai 25 a Kebbi.

A takardar da Manjo Janar E. I. Okoro ya rattabawa hannu ta ranar 3 ga Disamba, 2025; ya bayyana cewa, an kaddamar da dokar ne domin cike gibin da ake da shi a rundunar sojan kasa domin karfafa a tsaro a Najeriya.

Leave a Reply