Rundunar ’Yan Sanda ta dauka tsauraran matakan tsaro domin zaman lafiya lokacin bukukuwan Sallah a Legas

0 214

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta sanar da daukar tsauraran matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a lokacin bukukuwan Sallah, ciki har da tura jami’an musamman zuwa wuraren ibada, shakatawa da kuma wuraren da ake taruka.

Kakakin rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya ce an hada da Rundunar Gaggawa, ta Eko Strike Force da sauran sassan aikin leken asiri da hana ta’addanci da na’urar tona bama-bamai domin kare lafiyar al’umma.

An kuma sanar da tura motocin bindiga masu sulke da jami’an sintiri zuwa wuraren da ake ganin akwai yiwuwar aikata laifi, tare da gargadin cewa za a hukunta duk wanda ya karya doka.

Kwamishinan ’yan sanda ya bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani motsi da bai dace ba, tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai wajen tabbatar da tsaro a fadin Legas.

Leave a Reply