Gwamnatin Jigawa ta gano kusan ma’aikata 7,000 na bogi a wani shirin tantance ma’aikata da gwamnati ta aiwatar

0 836

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana gano kusan ma’aikata 7,000 na bogi a wani sabon shirin tantance ma’aikata da gwamnati ta aiwatar domin tabbatar da gaskiya da nagarta a tsarin albashi.

Kamar yadda Kwamishinar Kuɗi Hannatu Sabo ta bayyana, waɗannan ma’aikatan sun kasa halartar tantancewar ne wanda hakan ya sa aka cire sunayensu daga tsarin biyan albashi.

Ta ce wannan mataki ya bai wa gwamnati damar ɗaukar sabbin ma’aikata a karkashin shirye-shiryen J-Health, J-Teach da J-Agro, kana kuma jihar na daga cikin mafiya biyan albashi cikin lokaci da cikakken tsarin sabon albashi.

Leave a Reply