Rundunar yan sandan jihar Benue ta kama masu garkuwa da mutane 2 tare da kubutar da mutum guda daga hannun su

0 86

Rundunar yan sandan Jihar Benue ta kama masu garkuwa da mutane 2 tare da kubutar da mutum guda daga hannun su.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar Benue SP Anene Sewuese, ita ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a jiya.

A cewarta, Jami’an hukumar ne suka samu nasarar aiwatar da hakan a yankin Otukpa da ke karamar hukumar Ogbadibo, bayan sun samu labarin cewa yan bindigar sun sace wani mutum mai suna Raphael Okpe, da ke kyauyen Akere a lokacin da yake kokarin zuwa Gona.

Kakakin yan sandan ta ce Jami’an su, sunyi nasarar zuwa maboyar yan bindigar inda suka fatattake su bayan yin musayar wuta.

Sanarwar ta ce cikin mutanen da suka kama sun hada da Abdullahi Mohammed da Yusuf Saidu, sauran kuma sun gudu da Harbin bindigogi a jikinsu.

Haka kuma ta ce mutumin da yan sandan suka kubutar yana Asibiti yana karbar magani, sakamakon Harbin da yan bindigar suka yi masa a kafar sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: