A kalla manoma dubu 10 ne ‘yan Jihar Jigawa za su amfana da rancen kayan noma na RIFAN

0 99

A kalla manoma dubu 10 ne ‘yan Jihar Jigawa za su amfana da rancen kayan noma, karkashin kungiyar manoman shinkafa ta kasa RIFAN da hadin gwiwar shirin bunkasa noma na babban bankin kasa CBN wato Anchor Borrower.

Mukaddashin Kwamishinan Ma’aikatar gona da Albarkar kasa na Jihar Jigawa, Alhaji Ayuba Magaji Ayuba shine ya bada wannan tabbaci lokacin da shugabannin kungiyar manoman shinkafa RIFAN reshen karamar hukumar Birnin Kudu suka ziyarce shi a ofishinsa.

Mukaddashin kwamishinan ya ce manufar bada rancen shi ne domin tallafawa manoma da basu kwarin gwiwa wajen noma shinkafa mai yawa.

Magaji Ayuba ya ce baiwa manoman rance ya biyo bayan jajircewar Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na ganin manoman jihar Jigawa ba a barsu a baya ba ta fannin noma.

Tunda farko, a jawabinsa, sakataren kungiyar ta RIFAN reshen karamar hukumar Birnin Kudu, Malam Auwal Ado Sundumina, ya ce sun ziyarci mukaddashin kwamishinan ne domin taya shi murna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: