Kwamitin zakka na masarautar Dutse ya kaddamar da rabon zakkar kudade kusan biliyan biyu da rabi a gundumar Birnin Kudu

0 107

Kwamitin zakka na masarautar Dutse ya kaddamar da rabon zakkar kudade ta shekarar musulunci ta 1443 a gundumar Birnin Kudu.

An tara Zakkar kudi naira miliyan biyu da dubu 930 da aka rabawa mabukata dari biyu a gundumar Birnin Kudu.

A jawabinsa, mai martaba sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi ya hori Attajirai da manoma da su rinka fidda zakka domin tsarkake dukiyoyinsu.

A nasa jawabin Sa’in Dutse, Dr Mahmud Yunusa, yace gundumar Birnin Kudu ce ta zo na hudu wajen tattara zakkar kudi daga cikin gundumomin masarautar Dutse 28 da ake dasu.

Shima da yake jawabi, Hakimin Birnin Kudu, Sarkin Kudun Dutse Alhaji Garba Hassan Jibrin, yace zai cigaba da jajircewa wajen ganin masu hali suna bada zakka a gundumarsa.

A nasa jawabin, Shugaban karamar Hukumar Birnin Kudu, Alhaji Magaji Yusif Gigo, ya yabawa mai martaba sarkin Dutse bisa kishi da kuma kokarinsa na ganin ana karba da kuma raba zakka a masarautarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: