Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta kasa, Alhaji Sanusi Garba, ya ce ‘yan Najeriya za su shaida samun ingantacciyar wutar lantarki daga ranar 1 ga watan Yuli bayan sabunta kokarin masu ruwa da tsaki a bangaren.

Alhaji Sanusi Garba ya ba da wannan tabbacin ne a wata tattaunawa da manema labarai bayan taron masana’antar samar da wutar lantarki ta kasa karo na biyu da aka gudanar jiya a Legas.

Taron ya samu halartar manyan jami’an Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya, Da Kamfanin Watsa Wutar Lantarki TCN, Kamfanonin Samar da Wutar da kuma Kamfanonin Rarrabawa.

Ya ce hukumar ta kulla wata yarjejeniyar kwangila tsakanin masu ruwa da tsaki da za ta ba da tabbacin samar da wutar lantarki, watsawa da kuma rarraba wutar mai karfin megawatt dubu 5 ga masu amfani da wutar, farawa daga ranar 1 ga watan Yuli.

A cewarsa, kwantiragin ya rataya ne a kan dukkan bangarorin dake da alhakin samar da wutar lantarki, inda aka kayyade hukunci ga duk wanda ya sabawa tsarin yarjejeniyar.

Ya ce an jaddadawa dukkan masu ruwa da tsaki a bangaren cewa akwai hukunci idan suka sabawa yarjejeniyar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: