Sabon tsarin mafi karancin albashi zai fara aiki daga ranar 1 ga Afrilu, 2024

0 353

Gwamnatin tarayya a jiya Alhamis ta ce sabon tsarin mafi karancin albashi zai fara aiki daga ranar 1 ga Afrilu, 2024.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Idris Mohammed shine ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Abuja.

Ya ce mafi karancin albashi na Naira dubu 30 na yanzu zai kare ne a karshen Maris 2024.

Mohammed ya bayyana haka ne yayin nazari kan kasafin kudi na shekarar 2024 zuwa shekarar 2026 inda bayanai suka nuna cewa Gwamnatin Tarayya za ta kashe kudi sama da Naira tiriliyan 24kan albashi daga 2024 zuwa 2025, da kuma shekarar 2026.

Bayan cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Tinubu yayi a ranar 29 ga watan Mayun 2023, gwamnatin tarayya ta amince ta biya kowane ma’aikacin ta Naira 35,000 domin rage tasirin cire tallafin. Sai dai kungiyar kwadago ta dage kan cewa wannan karin na dubu 35 kamar kyauta ce ta wucin gadi ga ma’aikatan, inda ta kara da cewa ya kamata a sake duba mafi karancin albashi a shekarar 2024.

Leave a Reply

%d bloggers like this: