Sake fasalin kudi da gwamnatin da ta shude tayi ya durkusar da manoma a Najeriya

0 127

Gwamnatin tarayya ta ce tsarin sake fasalin takardar naira da gwamnatin da ta shude tayi ya sanya manoma cikin matsalar durkushewa.

Batun sake fasalin naira ya taso ne a zauren majalisar a lokacin da ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya fito domin kare kasafin kudin ma’aikatar sa.

A jawabin da ya gabatar a gaban kwamitin hadin gwiwa karkashin jagorancin Sanata Saliu Mustapha, ministan noman ya ce abin da aka fi mayar da hankali a kan kudirin kasafin kudin 2024 na fannin shi ne a samu wadatar abinci a kasa.

Ya ce abubuwa da dama da suka hada da rashin tsaro da manufar sake fasalin kudin Naira, wanda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya aiwatar kimanin shekara guda, ya jefa manoma cikin talauci tare da yin barazana ga samar da abinci a kasar. Kyari ya ce batun samar da abinci shine na daya a kan manufofi takwas na Shugaba Bola Tinubu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: