Sama Da Mutum 100 Ne Suka Mutu Sakamakon Zaftarewar kasa Da Ambaliya A Kasar Rwanda

0 84

Adadin wadanda suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ambaliya a kasar Rwanda ya haura sama da 100 sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar.

Kafar yada labaran kasar Rwanda ta bayar da rahoton cewa, ya zuwa yanzu mutane 109 ne suka mutu, 95 a lardin yammacin kasar da kuma 14 a lardin arewa.

Tun da farko, gwamnan lardin yammacin kasar ya shaida wa BBC cewa akalla mutane 50 ne suka mutu bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya ya mamaye yankin tsawon dare.

Gwamnan ya ce gidaje da dama sun fado kan mutane sannan akwai da dama da suka jikkata.

Ya ce manyan titunan lardin, da suka hada da sabuwar hanyar da ta bi ta tafkin Kivu, ba sa aiki saboda zaftarewar kasa.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto a wurare masu nisa inda adadin wadanda abin ya shafa zai iya karuwa.

Hukumar hasashen yanayi ta kasar Rwanda ta yi gargadin samun ruwan sama mai karfi a cikin wannan wata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: