Fadar Shugaban Kasa Tace Shugaba Buhari Ya Cika Alkawarukansa

0 82

Fadar Shugaban Kasa a jiya tace rashin san gaskiya ne ake kushewa da batawa da bayyana cewa kasarnan tana cikin mummunan hali a karshen mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari mai barin gado.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa daga babban mai taimakawa shugaban kasa akan kafafen yada labarai da huldar jama’a, Garba Shehu.

A cewar Garba Shehu, a wannan yanayin na zaman jiran tsammani bayan an kammala zabe da yawan yada labaran karya, abu ne mai kyau a bayyana hakikanin halin da ake ciki.

Yace kudirin tona asirin masu satar kudi na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karawa ‘yan Najeriya kwarin gwiwar bayyana barayi tare da kwatowa kasarnan daruruwan miliyoyin dalolin da barayin ‘yan siyasa suka sace suka boye a bankuna.

Garba Shehu yace hakazalika tattalin arzikin kasarnan ya samu cigaba sosai a zamanin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kakakin na shugaban kasa ya kara da cewa gwamnatin ta Buhari ta inganta rayuwar ‘yan Najeriya da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: