An Amince Da Biyan Gwamnatin Jihar Borno N16.7M Na Kudaden Da Ta Kashe Wajen Ayyukan Titunan Gwamnatin Tarayya

0 137

Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da biyan gwamnatin jihar Borno naira miliyan dubu 16 da miliyan 700 na kudaden da ta kashe wajen ayyukan titunan gwamnatin tarayya.

Babban mai taimakawa shugaban kasa akan kafafen yada labarai da hulda da jama’a a ofishin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, shine ya sanar da haka a jiya yayin da yake jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa akan takardar da shugaban kasa ya amince da ita yayin zaman ganawar majalisar zartarwa ta tarayya wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Laolu Akande ya ce ofishin kula da basuka na kasa zai gudanar da bincike akan halin da ake ciki dangane da bashi da kuma amincewar da aka samu daga majalisun kasa kafin a bada kudin ga gwamnatin jihar.

Ministan kimiyya, fasaha da kere-kere, Adeleke Mamora, yayin da yake jawabi ga manema labarai, ya sanar da cewa majalisar ta amince da daftarin cigaban fasahar kasa domin magance matsalolin sauyin yanayi da fara cin gajiyar bangarorin kasarnan da suka fi fuskantar barazanar lalacewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: