Samar Da Gidaje Ga Masu Yiwa Ƙasa Hidima A Jigawa Taimakon Kai ne – Jami’i

0 166

Jami’in hukumar yiwa kasa hidima reshen jihar Jigawa Alhaji Muhammad Ibrahim ya bukaci kungiyoyi masu zaman kansu da su samar da gidajen kwanan masu yiwa kasa hidima a jihar.

Ibrahim yayi wannan kira ne lokacin bikin yaye kashin farko na masu yiwa kasa hidima na 2109 rukunin A jiya alhamis.

Ya ce kiran ya zama wajibi domin samar da dukkanin wasu abubuwan walwala da jin dadinsu.

Ya ce akwai yawan masu yiwa kasa hidima da ya kai kimanin 2,500 da aka tura jihar wadanda suka hada da maza 1,600 da kuma mata 900.

Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya bukaci masu yiwa kasa hidimar su kasance wakilai na gari ga al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: