Sanadiyar ambaliya gidaje 200 sun rushe a garin Fataskum da ke jihar Yobe

0 401

A Najeriya,jihohin arewa maso gabashin ƙasar ne suka fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya da suka haddasa ambaliya da ta lalata daruruwan gidaje a Potiskum dake arewa maso gabashin ƙasar, kamar yadda hukumomin yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a daren jiya Juma’a zuwa wayewar garin yau Asabar.

Hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Yobe, inda garin yake, ta bayyana cewa gidaje 200 sun rushe.

A cewar wani jami’in hukumar, ba a samu asarar rai ba ko wandada suka samu raunika ba a dan tsakanin nan,duk da cewa gidaje da dama ne suka rushe.

Wani jami’in yankin mai suna Dauda Magaji ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa gidaje kusan 500 ne suka lalace, Jaridar RfI ce ta rawaito da hakan.

.

Leave a Reply