Dr. Sani Abdullahi Shinkafi ya bayyana cewa harin ya auku ne jim kadan bayan sallar Juma’a a hanyarsa ta dawowa gida, cewar Leadership.
Majiyoyi suka ce lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan sallar Juma’a inda wasu suka tare shi da makamai a Abuja da ke tsakiyar Najeriya.
Shinkafi ya ce maharan sanye suke da bakaken kaya, dauke da manyan makamai, sun tare motarsa kafin su kai masa hari, sannan suka tsere da mota kirar Prado baka.
Lamarin ya haifar da damuwa saboda barazanar da ake ta fuskanta daga ‘yan ta’adda da kuma yadda ake kai hari ga fitattun mutane a kasa.
Kungiyar ‘Patriots for the Advancement of Peace and Social Development’ ta ce yunƙurin kashe shi ya biyo bayan tsayin daka kan batutuwan tsaro a Zamfara.
“Wannan kokari ne na ganin baya na, amma ba zan bari barazana ta hana ni magana kan tsaro, zaman lafiya da cigaba ba.” – Cewar Shinkafi
Shinkafi ya bayyana cewa gidansa a Abuja ya rika samun kiran barazana a makon da ya gabata, kuma yana da alaka da wannan hari.