Sanata Barau I. Jibrin ya kaddamar da rabon tireloli 69 na takin zamani a jihar Kano

0 132

Mataimakin shugaban majalisar dattawan jihar Kano Sanata Barau I. Jibrin ya kaddamar da rabon tireloli 69 na takin zamani ga manoma a fadin kananan hukumomin jihar Kano 44.

A jiyaTalata ne aka fara raba buhunan takin zamani guda dubu 41,400 a kananan hukumomin Danbatta da Makoda dake yankin Kano ta Arewa, kamar yadda wata sanarwa daga kakakinsa Ismail Mudashir ta bayyana.

Shugaban ma’aikatan sa Farfesa Muhammad Ibn Abdallahi, wanda ya wakilci Sanata Barau, ya mika buhuna dubu 2,804 ga Danbatta da buhu 1,910 ga kananan hukumomin Makoda. 

Alhaji Dan Bayero, wanda ya yi magana a madadin mazauna Danbatta, ya nuna jin dadinsa ga Sanata Barau, bisa irin goyon bayan da yake ba su, yana mai nuni da shi a matsayin jagora mai kishin kasa da ya mai da hankali kan jin dadin mazauna Kano ta Arewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: