Tinubu ya amince da kafa ma’aikatar kiwon dabbobi

0 127

A makon da ya gabata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da kafa ma’aikatar kiwon dabbobi.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Talata a lokacin da yake kaddamar da kwamitin shugaban kasa kan sake fasalin kiwon dabbobi a zauren majalisar dokokin kasa.

Matakin da shugaban kasar ya dauka na kafa Ministan Dabbobi ya ci gaba da haifar da cece-kuce tasakanin masu ruwa da tsaki.

Kwamitin ya gabatar wa shugaban kasar shawarwari 21 da suka hada da samar da ma’aikatar kula da kiwo, da wasu matakai.

Bayan amincewar, shugaba Tinubu ya ci gaba da cewa gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin biyan kudin sayen filaye don tabbatar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: