Tinubu ya bukaci Majalisar Dattawa ta yi gyara a kan dokar kasafin kudin bana

0 104

Shugaban kasa Bola Tinubu, ya bukaci Majalisar Dattawa ta yi gyara a kan dokar kasafin kudin bana da ta harkokin kudade ta bara ta hanyar kara Naira tiriliyan 6.2 a cikin kasafin kudin bana.

A cikin wasikar da ya aike, shugaban ya bayyana cewar matakin ya dace da sashe na 58, karamin sashe na 2 na kundin tsarin mulkin kasar na 1999 da aka yiwa kwaskwarima.

Shugaban kasar ya gabatar wa majalisar dattawa da wannan kudiri domin ta yi nazari tare da zartar da shi.

Shugaba Tinubu ya kara da cewa ana bukatar yin kwaskwarima a kan dokar harkokin kudi ta 2023 ne, domin cazar haraji daga irin ribar da bankunan suka samu a hada-hadar musayar kudade kamar yadda bayanan hada-hadar kudadensu ta bara ta nuna.

Shugaban kasa ya ci gaba da cewar an yi haka ne domin samun kudaden gudanar da ayyukan raya kasa da bunkasa ilimi, kiwon lafiya da tsare-tsaren sanya walwala a zukatan al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: