Masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci daga kasar Isra’ila sun shawarci Najeriya da ta yi amfani da damar da take samu wajen inganta fasahar kere-kere domin bunkasa bangaren da ba na man fetur ba, musamman bangaren noma.
Wasu kwararrun kuma masana harkokin kasuwanci na kasar Isra’ila da suka yi jawabi a wajen taron shekara-shekara na dandalin kasuwanci na Najeriya da Isra’ila da aka gudanar a a jiya Laraba Abuja, sun ce abun da ke hana saurin bunkasa noma a Najeriya shi ne rashin iya tura sabbin fasahohin zamani don bunkasa samar da kayayyakin amfanin gona.
Da take jawabi a wajen taron, Jakadiyar Isra’ila a Najeriya, Michael Freeman, ta ce kasarta na alfahari da hada gwiwa da gwamnatin tarayya wajen bunkasa fannin tattalin arziki da kasuwanci.