Jam’iyyar Labour Party ta yi tir da tsige Sanata Ali Ndume daga matsayin mai tsawatarwa a majalissa

0 132

Shugabancin jam’iyyar Labour Party (LP) ya yi tir da tsige Sanata Ali Ndume daga matsayin mai tsawatarwa a majalissa saboda ya tsaya tsayin daka ga talakawan da ke shan wahala. 

jam’iyyar ta LP ta ce matakin ya nuna cewa a halin yanzu, “fadin gaskiya ga mulki” ya zama laifi a Najeriya.

Jam’iyyar Labour a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Obiora Ifoh, ya fitar, ta ce wulakancin da ‘yan majalisar dattawan karkashin jagorancin Godwin Akpabio suka yi wa Ndume na nuna irin salon mulkin kama-karya na jam’iyyar APC mai mulki.

jam’iyyar ta ce laifin da Ndume ya aikata shi ne nuna bajintar damuwarsa dangane da hauhawar tsadar rayuwa da karancin abinci, da kuma bayyanawa shugaban kasa irin matsananciyar yunwa da ake fama da ita a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: