Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Kano, Dakta Yusuf Kofar-Mata, ya rasa iyalansa guda uku sakamakon wata gobara da ta tashi a gidan sa da ke kofar-Mata a birnin Kano.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar jiya Laraba yayin da aka ce ‘yan uwa na barci.
Sai dai an ce kwamishinan ya tsira da kyar amma ya rasa ‘yarsa Maimuna da kanwarsa Khadija da kuma Juwairiyya.
An tattaro cewa gobarar ta lalata wasu kayayyaki masu daraja, amma babu wani rahoto a hukumance da zai iya tabbatar da hakan.
Da aka tuntubi kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Abdullahi Saminu, ya tabbatar da faruwar lamarin.