‘Yan bindiga sun kashe wani hakimi a jihar Kaduna

0 128

Wasu ‘yan bindiga sun kashe hakimin kauyen Kurmin- Kare, Ishaya Barnabas, tare dayin garkuwa da wasu mutane uku a karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindigar sun mamaye kauyen ne a kan babura inda suka nufi gidan basaraken suka harbe shi har lahira kafin su wuce gidan makwabcinsu inda suka yi garkuwa da wasu mazauna kauyen.

Ya shaidawa manema labarai cewa matasa ne suka hada kai suka kama daya daga cikin ‘yan fashin bayan ya fado daga kan babur.

Wanda ake zargi da aikata laifin, a cewarsa, an mika shi ga sojoji.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna, ASP Hassan Mansur, bai amsa kiran da aka masa ba don tabbatar da lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: