Mai Martaba Sarkin Gumel Alhaji Ahmed Muhammad Sani ya hori iyayen yara da sauran masu ruwa da tsaki a masarautarsa dasu kara sa ido sosai wajen zuwan yara makaranta da kuma tarbiyarsu.

Sarkin ya yi wannan bukatar ne a lokacin da babbar sakatariyar ma’aikatar ilmi, kimiyya da fasaha ta jiha, Hajiya Safiya Muhammad ta ziyarci fadarsa a Gumel.

Yace babu wata al’umma da za ta cigaba ba tare da ilimi mai inganci ba.

Sarkin na Gumel ya kuma yabawa ma’aikatar ilmi ta jiha bisa kokarinta na inganta alamurran ilimi a jihar nan tare da bada tabbacin masarautarsa na marawa kudirin gwamnati baya domin bunkasa harkokin ilmi.

A jawabinta Hajiya Safiya Muhammad tace ta kawo ziyarar ne domin neman tabarraki da kuma shawarwarin sarakuna iyayen kasa.

Tace gwamnatin jiha da dauki malamai dubu 4 da 500 aiki karkashin shirin koyarwa na J-Teach da za a tura makarantun firamare da kananan sakandire a fadin Jiharnan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: