GWAMNA BADARU YAYI AIKIN HANYA MAI TSAWAN KILOMITA 1,537 S FADIN JIHAR

A yunkurin sa na ganin ya samar da saukin sufuri, Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar yayi aikin hanya mai tsawan kilomita 1,537 a fadin jihar.

Gwamnan ya gaji akalla aikin hanyoyi masu tsawan kilomita 716 wanda kowannen su ya mataki daban daban na kammalawa, a inda ya bada sabbin ayyuka da suka tasamma kilomita 397 a shekarar 2016 da 2017 a inda aka kara bada wasu ayyukan a shekarar 2018 masu tsawan kilomita 410 da kuma kilomita 13.8 da akayi a Hadejia da Jigawa Dan Ali.

Auwal D Sankara (FICA)
Senior Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media (Babban Mataimaki na Musamman Ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafan sadarwa)

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: