Labarai

Shugaba Buhari ya jajantawa gwamnati da al’ummar kasar Kenya bisa rasuwar shugaban ‘yan adawar kasar na farko Mwai Kibaki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa gwamnati da al’ummar kasar Kenya bisa rasuwar shugaban ‘yan adawar kasar na farko Mwai Kibaki.

Shugaba Buhari, a wata sanarwa da ya fitar jiya ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya ce, Marigayi Kibaki ya kafa tarihin zama dan siyasa na farko da ya kawo karshen mulkin jam’iyya daya, bayan ta shafe shekaru 40 tana mulki a kasar, ya kuma kawo karshen ta a shekarar 2013.

Ya kuma ce Kibaki ya nuna cewa, dayin hakuri da juriya ne kadai, mutum zai iya cimma burinsa na rayuwa.

Garba Shehu ya ci gaba da cewa, mafi akasarin mutane suna barin gwagwarmaya ne bayan wasu ‘yan shekaru kadan, amma Kibaki ya tsaya kyam, ya kawo karshen mulkin jam’iyya daya data shafe shekaru 40 tana mulki a kasar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: