Gwamnatin Muhammadu Buhari tayi watsi da yaki da cin hanci da rashawa da ta yi amfani da shi wajen yakin neman zabe wanda ya bata mulki a 2015 – Femi Falana

0 52

Babban Lauyanan mai rajin kare hakkin Bil’adam, Femi Falana (SAN), ya zargi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari dayin watsi da yaki da cin hanci da rashawa da ta yi amfani da shi wajen yakin neman zabe wanda ya bata mulki a 2015.

Ya ce yin afuwa ga tsoffin gwamnonin jihar Taraba Jolly Nyame dana Plateau Joshua Dariye ya nuna gazawar gwamnati wajan yaki da cin hanci da rashawa.

Femi Falana ya bayyana hakan ne a mahaifar sa, a daidai lokacin da yake zantawa da manema a Alawe-Ekiti, a wajen bikin cika shekaru 10 na sarautar Oba Ajibade Alabi, dake Alawe. Ya ce kudaden da jam’iyyar APC da PDP suka kayyade a kan Naira miliyan 100 da miliyan 40 na siyan Fom din tsayawa takarar kujerar shugaban kasa ya sabawa doka, kuma shine Fom din tsayawa takara mafi tsada a duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: