Hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NIMet, ta yi hasashen samun hasken rana da gajimare daga ranar Litinin zuwa Laraba a fadin kasar.

Hasashen yanayi na da aka fitar jiya a Abuja ya yi hasashen cewa yankin arewa zai yi rana a yau tare da gajimare kadan tare da yiwuwar Tsawa da safe a sassan jihar Kebbi.

A cewar hukumar, za’asamu tsawa a sassan kudancin jihohin Borno, Kebbi, Kaduna, Gombe, Bauchi, Taraba da kuma Adamawa daga ranar Litinin zuwa Laraba da rana da kuma yamma.

Hukumar ta yi hasashen cewa yankin Arewa zai fuskanci hasken rana a ranar Talata da gajimare a safiyar ranar.

Hukumar ta kuma yi hasashen cewa za a yi Tsawa a wasu sassan Jihohin Kebbi, Jigawa, Bauchi, Gombe, Yobe, Taraba da kuma jihar Adamawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: