Labarai

A jiya ne al’ummar garin Gashu’a ta jihar Yobe sun shiga cikin firgici, sakamakon wata babbar fashewar wani abu da ya afku a garin

A jiya ne al’ummar garin Gashu’a, hedikwatar karamar hukumar Bade a jihar Yobe suka shiga cikin firgici, sakamakon wata babbar fashewa da ta afku a garin.

Gashu’a na da tazarar kilomita 188 daga Arewacin Damaturu babban birnin jihar Yobe kuma mahaifar shugaban majalisar dattawa mai ci ne Ahmad Lawan.

Lamarin ya faru ne a wani gidan giya da ke unguwar Abasha a cikin garin a lokacin da musulmi suke sallar magariba.

Lamarin dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan da mayakan Boko Haram suka kutsa wata Mashaya a cikin garin Geidam cikin dare, inda suka kashe mutane kusan goma sha daya.

Har ila yau, a cikin mako guda, wasu bama-bamai biyu sun tashi a wasu sassa na Jalingon jihar Taraba, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: