Labarai

Kungiyar dattawan jihar Katsina ta bayyana damuwarta kan aikin hanyar Kano zuwa Katsina da aka yi watsi da ita tsawon watanni uku da suka gabata

Kungiyar dattawan jihar Katsina ta bayyana damuwarta kan aikin hanyar Kano zuwa Katsina da aka yi watsi da ita tsawon watanni uku da suka gabata.

Sun yi kira ga Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola da ya umurci ’yan kwangilar da ke gudanar da aikin da su koma wurinsu su kammala.

Sakataren kungiyar dattawan, Alhaji Aliyu Sani Mohammed, ne ya yi wannan roko yayin wata tattaunawa da wasu ‘yan jarida a jihar.

A cewar Alhaji Aliyu, dan kwangilar ya kwashe dukkan kayan aikinsu daga wurin inda suka koma wani waje.

Titin mai hannu daya, wanda ake daga likafarsa zuwa mai hannu biyu domin saukaka zirga-zirgar ababen hawa a kan babbar hanyar,an kammala sama da kashi 65% kafin a yi watsi da shi sama da watanni uku da suka wuce.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN, ya bayyana cewa ’yan kwangilar sun dakatar da aikin hanyar ne saboda rashin biyan diyya ga masu kadarorin da ke yankunan da titin ya shafa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: