Shugaba Buhari Ya Taya ‘Yan Jarida Murnar Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida Ta Duniya

0 72

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya ‘yan jarida murnar zagayowar ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya da ake yi a duk ranar 3 ga watan Mayu a fadin duniya.

Bikin na bana ya cika shekaru 30 bayan shawarar da Majalisar Dinkin Duniya ta yanke na ayyana ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya.

Shugaban kasar ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar jiya a Abuja.

A cewar shugaban kasar, hakan kararramawa ce ga kwararrun ma’aikatan kafafen yada labarai, wadanda suke sadaukar da rayuwarsu domin fadakar da al’umma da kuma ilmantar da su.

Sai dai shugaba Buhari ya bukaci kwararrun ma’aikatan kafafen yada labarai da su ci gaba da kasancewa masu kishin kasa, da yin aiki domin hadin kan kasa, da kuma cin gajiyar ‘yancinsu na aiki ta kyakykyawar hanyar da ta dace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: