‘Yansandan Sun Kama Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa Da Aka Dakatar, Barista Hudu Yunusa-ari

0 80

‘Yansandan sun kama kwamishinan zaben jihar Adamawa da aka dakatar, Barista Hudu Yunusa-Ari.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda, Muyiwa Adejobi, shine ya tabbatar da kama Yunusa Ari a yau.
Yace ana cigaba da binciken wasu daga cikin mutanen da suka taka rawa a cece kucen da ya mamaye zaben.
Yunusa Ari ya haifar da cece kuce bayan ayyana Sanata Aisha Dahiru Binani ta jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaben duk da kasancewar ba a kammala tattara sakamakon zaben ba.
A wani batun kuma, Hudu Yunusa Ari, yace baya dana sanin ayyana sunan Aisha Dahiru Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan jihar.
Da yake jawabi a wata fira da sashen Hausa na BBC ya wallafa a yau, dakataccen kwamishinan zaben ya musanta cewa ya karbi cin hanci domin ayyanata a matsayin wacce ta lashe zaben.

Leave a Reply

%d bloggers like this: