Ministoci Suna Karban Albashin N942,000 Duk Wata Bayan An Cire Kudin Haraji – Chris Ngige

0 125

Ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige, ya sanar da cewa shi da sauran ministoci suna karbar albashin naira dubu 942 kowane wata bayan an cire kudaden haraji masu yawa.
Ministan ya sanar da haka yayinda ake ganawa da shi a gidan talabijin na Channels.
Ya kuma ce basu da alawus-alawus a matsayin ministoci kamar yadda ake rade-radi, in banda alawus na tafiya idan sun yi wata tafiyar aiki.
Ya kara da cewa kwanannan aka sake bibiyar alawus-alawus na tafiya da ministoci ke karba tare da na manyan sakatarori da sauran ma’aikatan gwamnati.
Da aka tambaye shi meyasa gwamnati ta kasa rage yawan marasa aikin yi a kasarnan wadanda suka karu zuwa kashi 33.3 cikin 100 a shekarar 2021, Chris Ngige yayi ikirarin cewa nauyin samar da aikin yi yana wuyan kamfanoni masu zaman kansu, ba bangaren gwamnati kadai ba.
Ya kuma dora alhakin rashin aikin yi akan raguwar masu zuba jari daga kasashen waje.

Leave a Reply

%d bloggers like this: